Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya zanta da shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas a birnin Beijing a yau Laraba.
Yayin ganawar tasu, shugaba Xi ya jaddada matsayar kasar sa, ta kasancewa cikin jerin kasashe na farko da suka amince da kungiyar ‘yantar da Falasdinawa ta PLO, da kasar Falasdinu, kuma Sin na matukar goyon bayan kare ‘yancin al’ummar Falasdinu, da dawo musu da hakkokin su na kasa.
Kaza lika shugaban na Sin ya gabatar da shawarwari guda 3, don gane da warware batun Falasdinu, yana mai cewa, Sin a shirye take, ta karfafa tsare-tsare, da hadin gwiwa tare da Falasdinawa, ta yadda za a ingiza matakan gaggauta cimma cikakkiyar nasarar warware batun Falasdinu baki daya kuma bisa adalci.
Daga nan sai shugabannin biyu suka bayyana kafa dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa, bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Falasdinu. (Saminu Alhassan)