Xi Zhongxun ya taba gaya wa dansa Xi Jinping cewa: “Komai girman ka a matsayinka na jami’i, kar ka manta da yi wa jama’a hidima yadda ya kamata, da tunawa da jama’a a da zuciya daya, da yin cudanya da jama’a, da kusantarsu.” Wadannan su ne kalmomin da mahaifinsa ya roka a wajensa dansa, kuma su ne abin da zuriyoyi biyu na ‘yan gurguzu suka gada.
Bisa la’akari da umarnin mahaifinsa, Xi Jinping ya kasance yana aiwatar da manufar “yi wa jama’a hidima da zuciya daya” tare hanyar gudanar da ayyuka a zahiri.
Zuriyoyi biyu ta mahaifi da da, tun daga “shugaban talakawa” zuwa “bawan jama’a” sun gaji nuna soyayya mai zurfi da kuma a zuciya ga jama’a. Ko a ina da kuma a wane lokaci jama’a su ne damuwarsu da karfinsu. (Ibrahim Yaya)