Daya daga cikin manufofin gwamnatin jihar Kano na inganta bangaren ilimi a jihar, gwamnan Injiniya Abba Kabir Yusuf ya amince da biyan kudin jarrabawar NECO ga daliban makarantun gwamnati 55,000 domin samun damar rubuta jarabawar ta kammala makarantar sakandire ta shekarar 2023 (SSCE).
Gwamnan jihar Engr. Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan wasu nasarorin da gwamnatinsa ta samu a cikin kwanaki 20 din farko da suka gabata a gwamnatinsa.
Injiniya Abba Kabir Yusuf ya bukaci daliban da suka amfana da su yi aiki tukuru don ganin kwalliya ta biya kudin sabulu.
A cewar Gwamnan, “A matsayinmu na gwamnati mai kishin jiha, dole mu tabbatar da cewa, kun samu damar ci gaba da karatuttukanku ba tare da wani shinge ba, sabida haka, mun amince nan take da biyan kudin jarabawar kammala karatun sakandire (NECO) ga daliban makarantun gwamnati 55,000 a fadin jihar nan.
“Ya kamata ku yi kokarin kuma ku jajirce domin ku fito da kyakkyawan sakamako da za ku iya farantawa jihar da ‘yan uwanku” Inji Gwamnan.
Ya kuma tabbatar wa al’ummar Kano cewa, gwamnatinsa za ta cigaba da lalubo manufofi da tsare-tsare na inganta harkar ilimi, domin ilimi shi ne ginshikin ci gaban kowace al’umma.