Injiniya Ahmad Salihijo Ahmad, Babban Daraktan Hukumar Raya Wutar Lantarki ta Karkara (REA), ya ce, Gwamnatin Tarayya na kokarin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana ga ‘yan Nijeriya domin rage radadin cire tallafin mai ga ‘yan kasuwa da gidaje.
Ahmad, wanda ya bayyana hakan Jim kadan bayan kammala duba aikin samar da makamashin wutar lantarki mai amfani da hasken rana a Babbar kasuwar kasa da kasa ta Ayegbaju, Osogbo, ya ce Gwamnatin tarayya ta hanyar REA, na samar da makamashi masu amfani da hasken rana sabida karancin wutar lantarki da ake fuskanta.
Ya kuma bayyana cewa, manufar shirin shi ne samar da tsaftataccen makamashin hasken rana ga ‘yan Nijeriya don rage wa ko kawar da amfani da janareta mai fitar da hayaki wanda ka iya haifar da matsala ga kiwon lafiyar dan Adam (Carbon monoxide).
Ya ce aikin samar da makamashi mai amfani da hasken rana a Kasuwar Ayegbaju ya kai kusan kashi 95 cikin 100 kuma ana sa ran zai samar da wutar lantarki mai girman 30kwp.