Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa jihar za ta sake gina tsohuwar ganuwar Kano da burbushin gine-ginen da aka rushe a jihar, inda ya ce tuni an fara aikin sake gina ganuwar.
Yusuf ya bayyana hakan ne a lokacin da yake rangadi a wasu wuraren da aka rushe a cikin babban birnin Kano a ranakun karshe na makon da ya gabata.
Gwamnan a cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun babban sakataren yada labaransa, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya bayar da tabbacin cewa za a yi amfani da burbushin gine-ginen da aka rushe domin sake gina ganuwar jihar.
Sai dai ya yi gargadin cewa: “Mutanen da ba su da wata alaka da wuraren da aka rusa, ba a bukatar ganinsu a wuraren, kuma an umurci jami’an ‘yansanda da jami’an tsaron farin kaya na Nijeriya (NSCDC) da su samar da tsaro a wuraren da aka ruguza don kiyaye wuraren daga masu kutse”.
Har ila yau, Gwamnan ya yi kira ga mutanen Kano nagari da su ci gaba da bin doka da oda tare da kai rahoto ga jami’an tsaro kan duk wani abu da ka iya barazana ga harkar tsaro domin ci gaba da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar ta Kano.