Wani jarimi da aka bayyana sunansa da Ifeanyi wanda ya arce daga sansanin ‘yan bindiga a dajin Kagarko da ke karamar hukumar a jihar Kaduna ya kubuta daga duk da harbin da aka masa a kafa.
Ifeanyi, ya mallaki wani babban shago ne a wata kasuwa a garin Kagarko, ‘yan bindigar sun yi garkuwa da shi ne a makon da ya gabata a gidansa da ke garin Kagarko.
Wani mazaunin garin mai suna Shuaibu Bala ne ya tabbatar da kubutar Ifeanyi bayan harbinsa a kafa. Kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Shuaibu ya kara da cewa, duk da harbin da masu garkuwar suka yiwa Ifeanyi a kafa, ya yi namijin kokarin sake arcewa daga hannun ‘yan bindigar.
Ya bayyana cewa, wasu manoma ne da ke aiki a gonakansu suka sanar da wasu ‘yan sintiri da ke yankin, inda suka zo suka dauki Ifeanyi suka kai shi Asibiti.
An yi kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yansanda na jihar Kaduna kan lamarin amma hakan ya ci tura.