Gwamnan Jihar Katsina Umaru Dikko Radda, ya kira wani taro na masu ruwa da tsaki kan harkokin tsaro domin tattauna hanyoyin da ya kamata a bi domin magance matsalar tsaro a jihar.
Masu ruwa da tsakin sun hada da shugabannin kananan hukumomin da matsalar tsaro ta shafa, ‘yan majalisar dokokin jihar, shugabannin tsaro, masu rike da sarautun gargajiya da malaman Addini a jihar.
Da yake magana a wajen taron, Gwamna Radda ya ce an kira taron ne domin zakulo hanyoyin magance kalubalen tsaro a jihar.
Gwamnan ya kara da cewa gwamnatinsa ta dauki aniyar kafa wata cibiya ta musamman a cikin al’umma mai suna ‘Community Watch’ da za ta nemo matasa ta ba su horo na musamman don su ba da gudunmuwa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar yankunansu daga hare-haren ‘yan bindiga.
Wannan cibiya, za ta hada matasan da jami’an tsaro a dukkanin kananan hukumomi 34 da ke jihar wajen inganta tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.
Radda, ya ce zai gabatar wa majalisar dokokin jihar kudiri domin kafa doka ta musamman da za ta sa a samu raguwar aikata ayyukan assha a cikin al’umma, musamman a yankunan karkara na jihar.
Inganta tsaro na daga cikin alkawuran da gwamnan ya dauka a lokacin da yake yakin neman zabensa.