Mamallakin kungiyar kwallon kafa ta Chelsea dake Ingila Todd Boehly ya shirya tsaf domin sayen kungiyar kwallon kafa ta Strasbourg dake buga gasar Ligue1 ta kasar Faransa.
Boehly wanda ya saye Chelsea bara akan kudi £4.5 bn ya shirya mallakar kashi 94 na kungiyar inji shugabanta Marc Keller.
Keller ya kara da cewa mun dade muna jiran wannan rana wadda wani hamshaki zai saye Strasbourg domin cigaba da gudanar da ita kamar yada muka fara, Strasbourg ta kare a mataki na 15 a gasar Ligue1 ta kasar Faransa a bana
Hamshakin dan kasuwa na kasar Amurka Yodd Boehly ya saye Chelsea a hannun Roman Abromavic bara,lokacinda aka tursasa Abromavic sayar da ita
A zaman da Boehly yayi a matsayin shugaban Chelsea ya kori koci biyu yayinda kungiyar ta kare a mataki na 12 a gasar Firimiya
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp