Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce sabbin rajistar masu kada kuri’a da ake ci gaba da yi a fadin Nijeriya ta Kai Miliyan 10,487,972 a dai-dai karfe 7:00 na safiyar ranar Litinin, 27 ga watan Yuni.
Hukumar a cikin rahotonta na mako-mako akan cigaban Sabuwar Rajistar zabe wanda aka fitar a ranar Litinin a Abuja, ta bayyana cewa masu kada Kuri’a Miliyan 8,631,696 ne suka kammala rajistar.
Ta bayyana cewa masu kada Kuri’ar, Mutum Miliyan 3,250,449 sun kammala rajistar ne ta hanyar yanar gizo, yayin da 5,381,247 suka je rumfuna Daban-daban don yin rajistar.
Daga cikin wadanda suka kammala rajistar, akwai Maza Miliyan 4,292,690 sai Mata Miliyan 4,339,006. Daga cikin wadannan adadi, 6,081,456 matasa ne, yayin da 67,171 nakasassu ne.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa INEC ta samu jimillar mutane Miliyan 23,560,043 da suka hada da masu neman sauya akwatin zabe da wadanda suke neman sauyin katin nasu Katin da masu neman gyaran bayanan su a katin zaben.