Kamfanin da ya mallaki manhajar Whatsapp ya ce yanzu mutane za su iya gyara kuskuren da suka yi a sakon da suka tura, kamar yadda akan iya yi a wasu manhajojin irin su Telegram da Facebook.
Kamfanin ya ce za a iya gyara kuskuren da aka yin ne a cikin minti 15 bayan tura sakon. Wato idan sakon ya wuce minti 15, to sakon ba zai gyaru ba.
Whatsapp manhaja ce mallakar kamfanin Meta na Amurka, wanda shi ne ya mallaki Facebook da Instagram.
A cikin makonni masu zuwa ne za a samar da tsarin iya gyara kurakuran da mutane biliyan biyu da ke amfani da Whatsapp a fadin duniya.
Indiya ce kasa mafi yawan al’umma da ke amfani da manhajar, inda indiyawa miliyan 487 ke amfani da ita.
Masu manhajar sun ce “Za a iya gyara kuskuren da aka yi wajen rubutu ko a yi karin bayani a kan sakon, wannan wata dama ce da za ta ba ku ikon sarrafa sakonninku yadda kuke so.”
Sakon ya kara da cewa hanyar da za a bi wajen gyara kuskuren ita ce “A danna kan sakon na tsawon dakiku, sai a zabi ‘Edit’ daga cikin sakon da zai fito, ana iya yin haka a cikin minti 15 bayan tura sako.”
Sai dai za a nuna wa wanda aka tura wa sakon din cewa an yi gyara a sakon.
Amma ba za a nuna masa tsohon bayanin ba da aka gyara din ba.
A wancan lokacin kamfanin na facebook ya ce ya samar da tsarin ne saboda mafi yawan masu amfani da shi suna shiga ne ta wayoyinsu na hannu, abin da ke sa suna yawan yin kuskure wajen rubutu.
A bara ne ita ma manhajar Twitter ta fito da tsarin yin gyara a sakonnin da aka yi kuskure wajen rubuta su, inda ake iya yin gyaran cikin minti talatin bayan wallafa sako.
Sai kuma jan hankali game da amfani da GB Whatsapp. Masu amfani da GB Whatsapp idan ba su daina ba, wayar za ta daina yin kowane irin whatsapp kwata-kwata. A mako mai zuwa za a ji cikakken bayani.