Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana yayin taron manema labarai na yau Litinin cewa, bisa gayyatar kasar Sin, mataimakiyar sakatare janar na MDD Amina Mohammed, ta fara ziyarar aiki a kasar Sin daga jiya Lahadi. Ta ce bangarorin biyu za su mayar da hankali wajen musayar ra’ayi mai zurfi kan hadin gwiwar Sin da MDD, da batun samar da ci gaba mai dorewa, da kyautata tsarin samar da kudin gudanar da ayyuka, da batun sauyin yanayi, da ma sauran wasu batutuwa.
Game da batun bibiyar asalin cutar COVID-19 kuwa, Mao Ning ta ce kamata ya yi Amurka da gaggauta daina siyasantar da batun, da amfani da shi a matsyain makami, kana ta daina bata sunan sauran kasashe. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha)