Yayin da al’ummar musulmi a fadin duniya ke gudanar da shagulgulan babbar sallah ta bana, ita ma kungiyar musulmin kasar Sin ta gudanar da liyafar bikin babbar sallah a jiya Laraba.
Mataimakin babban jami’in sashen ayyuka na musamman a kwamitin kolin JKS Chen Xiaojiang, da takwaransa Chen Ruifeng, wanda kuma shi ne darakta a hukumar lura da harkokin addinai ta kasar Sin na cikin mahalarta bikin.
Da yake tsokaci yayin bikin da aka shirya, mataimakin shugaban kungiyar Adiljan Haj Kerim, ya gabatar da sakon gaisuwa da fatan alheri ga daukacin musulmin kasar Sin. Ya kuma bukace su da su kara azama wajen kiyaye dokokin addini bisa yanayin kasar Sin, da salo da tsarin gurguzu na al’ummar ta.
Taron ya hallar baki masu yawa, ciki har da jakadun kasashen musulmi sama da 40, da ma’aikan musulmi ‘yan kasashen waje dake birnin Beijing, da jami’ai daga gwamnatin tsakiya da na birnin Beijing, tare da wakilan al’ummar musulmi sama da 180 daga sassa daban daban a birnin. (Mai fassara: Saminu Alhassan)