- Yadda Muka Samu Nasarar Hana Cin Kasuwar Madalla A Titi
- Mata Ne Za Su Zama Sakatarorin Kananan Hukumomi Da Mataimakansu A Neja
A kwanan baya, Gwamnan Jihar Neja, Umar Bago ya kai ziyara ta musamman ga Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu a fadarsa da ke Abuja. Jim kadan bayan ganawarsu, wakilinmu na fadar shugaban kasa, JONATHAN INDA-ISAIAH ya tattauna da shi a kan makasudin ziyarar da kuma wasu abubuwa da suka shafi sha’anin tsaro a Jihar Neja. RABI’U ALI INDABAWA ya rubuta mana tattaunawar kamar haka:
Mene ne takamaimai ya kawo ka fadar shugaban kasa a wannan lokacin?
Na farko dai na zo na taya murna gaba ki daya, kuma mu kara jaddada masa cewa in Allah ya yarda gwamnoni musamman jam’iyyar APC za mu yi aiki da shi, kuma majalisa inda na fito kafin na zama gwamna, mun je mun kaddamar da zabe mun gaya musu baya kuma Allah ya sa abin da aka nema an samu. Amma bayan haka na zo ne da abu guda biyu, na farko mu Arewa ta Tsakiya muna kara kira da babbar murya cewa muna neman alfarma ga mai girma shugaban kasa a kara duba mu da idon rahma, bayan haka Ibtila’i na rashin tsaro da ya yi mana kakaka mun zo domin mu nemi taimako daga wurin gwamnatin tarayya don a samu waraka a wannan harka.
An ganka kana rushe-rushe na wasu Hukumomi da aka ba da wa’adi me hakan yake nufi da wace kafa kenan ka fara da ita a Jihar Neja?
Na farko dai gwamnatinmu ba za mu yarda da zalunci ba, saboda haka mutane ba za su yi gini a kan hanyar ruwa ba ko hanyar wuta, wannan ba za mu yarda ba. Ko ofishin ‘yansanda da muka rusa mun rusa ne saboda yana kan hanyar ruwa. A baya idan an kunna ruwa sai ‘yansanda su hana kamfanin ruwa bude ruwa, kuma talaka yana son ruwa. Da muka samu wannan labarin muka fara da shi, wadansu kuwa karfa-karfa a baya sun zo sun gina gidajen mai a tsakanin mutane ba su da mu da cewa zai damu mutane ba, saboda haka suma din mun rufe su kuma mun kwace takardunsu kuma za mu rusa su gabaki daya, kuma wadannan filayen da muka karbe filaye ne na gwamnati, kuma asalin tsari na yadda za a tafiyar da jihar Neja, wannan wuraren shugabannin da suka gabata su kebe su ne saboda al’umma, saboda haka mutane sun zo suna so su handama ko sun karbe don suna dama, to shi ne Allah ya bamu dama mu juya alkiblar.
Fatan da ‘yan Jihar Neja ke da shi ita ce matsalar tsaro da yake addabarsu ko menene kake da shi ganin cewa hakan ya zo karshe?
To a cikin shirye-shiryen da muke da shi, na farko Jihar Neja tana daga cikin jihar da ta fi kowacce girma a fili, to yawancin dajikanmu ba a noma a ciki, to muna kira ga gwamnatin tarayya ta hada hannu da mu mu nome wadannan dazuka, na farko kenan. Na biyu kuma kafin a kai ga wurin muna neman taimakon ‘yan sanda da sojoji su zo su higa wadannan dazukan su zo su taya mu aiki don mu samu zama lafiya.
Wane shiri kake da shi game da mata?
Wannan gwamnatin ta mat ace, kuma muna so mu ba wa samari da mata dama sosai a wannan gwamnatin, alal misali sakatarori na karamar hukamar Neja gabaki daya su 25, in Allah yarda za mu maida su mata, don haka in za a kara zabe na kananan hukumomi za mu mayar da mataimakan shugabannin kananan hukumomi duka mata. Bayan haka akwai kwamishinoni da yawa da zamu dauka mata da kuma masu ba da shawara mata da wasu mukamai. Kamar nan da kwana kadan za a ji na ba da mukamai na mata su zan ma fara ba wa kafin na fara ba wa maza.
Wannan ne karon farko da ka zama gwamna, kuma kakakin majalisar jiharka shima shi ne zuwansa majalisa karonsa na farko, ya za ku tafi da wannan mulki?
Allah, Allah muka sa a gaba shi ne zai mana jagora shi ne ya kawo mu, amma ina so ka gane cewa ba yanzu ba fa muka fara aikin gwamnati, shekara 12 na ajiye akwati an zabe ina majalisar tarayya, saboda haka maganar mulki da kuma tafiyar da al’amuran mulki in sha Allahu ba bako bane a gare mu sai dai zama gwamna bako ne a gare mu, kuma kakakin majalisa da muka zaba shi ma ba bako bane a gwamnatance, kuma in Allah ya yarda Allah zai mana jagora.
Dangane da hanyar kasuwar Madalla din nan da kowa zai shiga Abuja sai ya kan samu matsaloli ranar Alhamis ranar kasuwa, amma tun makonni uku da wuce an gyara wurin, ta yaya ka samu wannan nasara?
Na farko mun riga mun haramta a gwamnatance cin kasuwa a kan titi, kuma kowa ya yi za mu kama shi mu ci shi tara, bayan haka talaka ma ko masu cin kasuwa a wurin suma sun koka kan wannan al’amari na cin kasuwa a kan titi. Amma dai yanzu muna kokarin fili da aka kebe, na wannan kasuwa din mun kira manya-manyan kamfaninnika masu zaman kansu na gine-gine wadanda mutane Jihar Neja su ne suke wadannan kafanoni, kamar Urban Shelta, Barain and Harmer, Kos Group, Modern Shelter, Bilad da sauransu. Mun kira sum un ce su zo mu hada karfi da karfe don a samu wannan mafita, in Allah ya yarda nan da kwana kadan za a gina kasuwanni da yawa, birnin Suleja za mu mai da shi babban birni na cin kasuwa na Arewa gabaki daya.