Mahukuntan kula da gine-gine a kasar Brazil sun ci tarar Neymar, bayan da karo biyu yana kin bin umarnin dakatar da wasu gine-gine da yake yi a gidansa kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Tsohon dan kwallon na Barcelona yana da katafaren gida mai dauke da kayayyakin alfarma da kawa a Rio de Janeiro. Sai dai tun farko dan kwallon tawagar Brazil da Paris St Germain din na fuskantar biyan wata tarar da ta kai fam miliyan daya.
Hakan ya biyo bayan da mahukuntan suka ce sun gano Neymar yana gina wani kududdufin yin wanka da wani tsibiri a gefensa a garin Mangaratiba, sannan Mahukuntan sun dakatar da ci gaba da aikin, inda wasu kafar yada labarai a Brazil suka ce sai dan kwallon ya gayyaci mutane biki da a wannan kududdufin.
Ranar Asabar mahukuntan suka sake kai ziyara gidan Neymar suka ga yadda aka yi biris da umarnin da suka bayar tun farko kan a dakatar da aika-aikace kuma wakilan Neymar har yanzu ba su ce komai ba, bayan da kamfanin dillacin labarai na AFP ya tuntube su.
Neymar mai shekara 31, yana jinya bayan da likitoci suka yi masa aiki a kafarsa ta hagu tun a watan Maris a Doha Katar kuma rabon da dan wasan ya buga wasa tun cikin watan Fabrairu, har ma ana ta rade-radin cewar da-kyar idan zai iya ci gaba da buga wasa a PSG a kakar da za a fara.
Neymar ya sayi katafaren gidan da ke garin Mangaratiba a shekarar 2016, wanda ke dauke da gine-ginen alfarma da kaya na kawa kuma idan yaje hutu Brazil yana zama a gidan.