Rundunar ‘yansandan jihar Ondo ta cafke masu garkuwa da malamin addinin musulunci, Alli Ibrahim Bodunde, wadanda aka yi garkuwa da shi a unguwar Uso da ke karamar hukumar Owo ta jihar a makonnin da suka gabata.
Wadanda ake zargin sun yi garkuwa da babban limamin unguwar Uso mai shekaru 67 a gonarsa da ke sansanin Asolo. An sake shi ne bayan da Jama’ar yankin suka biya kudin fansar naira miliyan 2.
Da yake gabatar da wadanda ake zargin a hedikwatar ‘yan sanda da ke titin Igbatoro a Akure, babban birnin jihar, Kakakin ‘yan sandan Jihar, Funmilayo Odunlami-Omisanya, ya ce wadanda ake zargin su ne Muinah Mohammed mai shekaru 19 da Aisha Bello mai shekaru 20 da kuma Isah Bello mai shekaru 40.
Odunlami-Omisanya ya ce; “A ranar 18 ga watan Yuni, 2023, wata Misis Bodunde da misalin karfe 6 na yamma ta je ofishin ‘Yan sanda na Uso inda ta yi korafin cewa mijinta, Alli Ibrahim Bodunde ya je gona kuma ya kamata ya dawo da misalin karfe 2 na rana amma abin takaici har yanzu bai dawo ba.
“Lokacin da ’yan uwa ba su gan shi ba, sai suka tura mutum biyu zuwa gona domin nemansa.
“Lokacin da suka isa gona sai suka hadu da motarsa da wayarsa amma ba su gan shi ba.
“Kuma nan take aka kai rahoton lamarin, ‘yan sanda suka shiga aikin, inda a karshe aka sako mutumin.
“Amma a dalilin binciken mun gano cewa mutumin da ake magana a kai shi ne babban limamin al’ummar Uso.
“Ta hanyar jami’an leken asirinmu, mun samu nasarar cafke wadanda ake zargin kuma a karshen binciken za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.