Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya amsa wasikar da daliban kasashen waje dake karatun digiri na 2 a fannin aikin binciken kudi, a jami’ar Nanjing Audit ta lardin Jiangsu suka rubuta masa, inda a cikin martanin wasikar, ya ja hankalin su da su ba da gudummawar karfafa kawance da hadin gwiwar kasashe daban daban.
Xi, ya yi kiran ne a jiya Talata, cikin amsar wasikar daliban, yana mai cewa, bayan kwashe tsawon shekaru ana aiki tukuru, tsarin binciken kudi mai halayyar musamman na Sin ya kafu, don haka ya yi fatan daliban za su kara azamar bunkasa musaya, da koyi da juna tsakanin su da takwarorin su daliban kasar Sin, su kuma dauki fannin da suke karatu a matsayin damar kara fahimtar kasar Sin, da ba da gudummawar zurfafa abota, da hadin gwiwa tsakanin sassan kasa da kasa.
Tun bayan kaddamar da kwas din a shekarar 2016, tsangayar koyar da ilimin binciken kudi na kasa da kasa ajin digiri na 2, a jami’ar Nanjing Audit, ta horas da dalibai sama da 280, wadanda ke aiki a hukumomin kasashen duniya 76, dake cikin shawarar ziri daya da hanya daya. (Saminu Alhassan)