Jiya Talata, aka gudanar da taron koli na kungiyar SCO ta kafar bidiyo, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da jawabin cewa, ya kamata mambobin kungiyar su hada kansu don tabbatar da taka rawar gani wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankalin duniya.
To ta yaya za a tabbatar da taka rawar gani ga bunkasuwar duniya?
Shugaba Xi Jinping ya amsa da cewa, tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da samun bunkasuwa da hada kai don cin moriya tare abubuwa ne da kowa ya amince da su, kana ba wanda zai iya hana. Hakan ya sa, Xi Jinping ya gabatar da ra’ayin daukar matakai masu dacewa don kara karfin kungiyar, ta yadda mambobinta za su kara amincewa da juna da hada gwiwa da tabbatar da tsaronsu na bai daya da kuma cimma nasarorin hadin kai da kara cudanyar al’umomminsu.
Ban da wannan kuma, Xi Jinping ya yi kira ga mambobin da su yayata muradun bil Adama na bai daya wato zaman lafiya da bunkasuwa da daidaito da adalci da demokuradiyya da ‘yanci, ta yadda za a tabbatar da burin zamanintar da al’ummar duniya ta hanyar cimma wadannan muradun. (Amina Xu)