Kimanin motoci miliyan 3.13 masu amfani da sabon makamashi aka yi wa rejista a rabin farkon bana a kasar Sin, adadin da ya karu da kaso 41.6 a kan na bara, wanda kuma ya kai matsayin koli.
Wannan ya kawo jimilar adadin motoci masu amfani da sabon makamashi a kasar, zuwa miliyan 16.2 a karshen watan Yuni, wanda kuma ya dauki kaso 4.9 a jimilar motoci a kasar.
Bisa kididdiga, an yi wa motoci miliyan 16.88 rejista a kasar Sin a rabin farko na bana, wanda ya kawo adadin motocin da aka mallaka a kasar zuwa miliyan 426, ya zuwa karshen watan Yuni.
A jimlace, biranen kasar Sin 88 na kasar Sin na da motoci sama da miliyan 1 a karshen watan Yuni, karuwar 7 idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara. Kana adadin motoci a biranen Beijing da Chengdu, ya zarce miliyan 6. (Fa’iza)