Uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta karyata rahoton da ke ikirarin cewa ta bayar da umarnin rufe dakin ibada na Aso Rock Chapel da ke fadar shugaban kasa a Villa, Abuja.
A cewar wata sanarwa da mai ba ta shawara ta musamman kan harkokin yada labarai, Busola Kukoyi ta fitar.
- Gwamnan Kebbi Ya Kori Hadiminsa Kan Wallafa Wani Sako A Kafafen Sada Zumunta
- Kotu Ta Hana INEC Gurfanar Da Kwamishinan Zaben Adamawa
Ta ce, babu lokacin da uwargidan shugaban kasar ta bayar da wannan umarni, inda ta kara da cewa dakin ibadar na ci gaba da aiki saboda har yanzu akwai taron tattaunawa na mako-mako da ake yi a cikinsa.
“An ja hankalinmu kan wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta game da batun rufe dakin taro na As Rock Chapel da uwargidan shugaban Nijeriya, Sen Olurermi Tinubu aka ce ta yi.
“Muna so mu bayyana cewar wannan kirkira ce kuma uwargidan shugaban kasa ba ta taba ba da umarnin a rufe dakin ibadar ba.
“A yanzu haka ana gudanar da taron mako-mako a Chapel,” in ji sanarwar.
Duk da haka, har yanzu shugaban kasa bai nada wani limamin cocin ba bayan ficewar limamin cocin na karshe.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp