A kokarinsa na shawo kan tashin gwauron kayan masarufi a Nijeriya, shugaba Tinubu ya bayar da samar da abinci da kaddamar da wasu matakain gaggawa don tabbatar da an samar da wadattacen abinci ga ‘Yan Nijeriya.
Mai ba shugaban kasa shawara kan a kafafen sadarwa, Dele Alake, ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai a ranar Alhamis.
- Tinubu Ya Nemi Majalisa Ta Tabbatar Da Nadin Sabbin Hafsoshin Tsaron Nijeriya
- Cire Tallafin Fetur: Tinubu Na Neman Sahalewar Majalisar Wakilai Don Samar Da Kudaden Rage Radadi
Alake ya ce, duba da samun hauhawar farashin kayan abinci, ya ce shugaba Tinubu ya ba da umarnin tallafa wa masu karamin karfi.
Alake ya ce, shugaban ya bayar da umarnin samar da wadattacen abinci don samun saukin rage radadin cire tallafi.