Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya yi watsi da zarge-zargen da kungiyar tsaro ta NATO ta yi wa kasarsa.
Zhang Jun ya shaidawa Kwamitin Sulhu na MDD cewa, sanarwar bayan taron NATO a Vilnius na Lithuania, cike take da ra’ayin cacar baka da nuna wariya. Haka kuma ta keta gaskiya tare da zarge-zarge marasa tushe da dacewa kan kasar Sin, yana mai cewa, Sin na adawa da zarge-zargen na munafurci.
Ya ce Sin kasa ce mai rajin tabbatar da zaman lafiyar duniya, kuma mai bayar da gudunmuwa ga ci gaban duniya, haka kuma mai kare tsari da odar duniya. Ya ce idan ana batu na tsaro da zaman lafiya, to, kasar Sin na tinkaho da nasarorin da ta cimma a bangaren fiye da sauran manyan kasashe. Ya ce kasarsa ba ta taba kutsawa kasashen duniya ba, ko tunzura wasu shiga yaki ba, ko gudanar da wasu matakan soji a fadin duniya, ko yi wa wata kasa barazana ta karfi, ko kakaba akidunta kan wata ko ma tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasashe ba.
A cewar Zhang Jun, har kullum, kasar Sin ta kasance mai nacewa ga neman cikakkiyar zaman lafiya na bai daya bisa hadin gwiwa, kuma mai dorewa. Yana mai cewa, a shirye Sin din take, ta hada hannu da kasashen duniya wajen gina tsarin tsaro mai inganci da daidaito da dorewa, ta hanyar tattaunawa da hadin gwiwa, ta yadda za a samar da zaman lafiya mai dorewa na bai daya. (Fa’iza Mustapha)