Ambaliyar ruwan ta ci yankuna da dama a Jihar Katsina sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da yi matukar tabka barna a wasu wurare.
Mataimakin gwamnan Jihar Katsina, Malam Faruk Lawal Jobe ya ziyarci wasu yankuna da ambaliyar ruwa ta shafa sakamakon ruwan sama da aka samu a cikin birnin Katsina.
- Gwamnatin Neja Ta Bayar Da Umarnin Kawo Karshen Matsalar Tsaro
- An Yi Bikin Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Mika Asibitin Zumunta Na Sin Da Equatorial Guinea
Wuraren da aka ziyarta sun hada da hanyar gadar kasa da ke Kofar Kaura da Tudun Katsira da kuma Kofar Marusa. Ziyarar na da nufin tantance yankunan da lamarin ya shafa.
Ya ce gwamnati za ta samu injiniyoyi daga ma’aikatar ayyuka domin tantance abubuwa da suka lalace da kuma daukar matakin kare afkuwar irin wannan iftila’i nan gaba. Ya jajanta wa wadanda lamarin ya rutsa da su, inda ya roki Allah ya kare afkuwarsa a nan gaba.
Mataimakin gwamnan ya nanata kudurin gwamnati wajen tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a lokacin damina da kuma bayan damina.
Haka kuma mataimakin gwamna ya gudanar da taro na musamman da jami’an ma’aikatar ayyuka da na hukumar SEPA da na hukumar bayar da agajin gaggawa ta jiha da kuma wakilin kamfanin da ya gudanar da aikin gadojin kasa na Kofar Kaura da Kofar Kwaya.
Ya ce taron zai tattauna ne a kan matakan da za a dauka domin shawo kan lamarin.