A yammacin yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna da takwaransa na kasar Aljeriya Abdelmadjid Tebboune dake ziyarar aiki a nan birnin Beijing.
Xi Jinping ya yi nuni da cewa, Sin tana son yin hadin gwiwa da Aljeriya wajen gaggauta aiwatar da sakamakon da aka cimma a taron koli na farko na kasar Sin da kasashen Larabawa, da karfafa hadin gwiwa a tsarin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, da ma ingiza kafa kyakkyawar makomar al’ummar kasashen biyu da ma Sin da Afrika ta bai daya a sabon zamani, da kara samun sulhuntawa da hadi kai a dandalin kasa da kasa, ciki har da MDD, ta yadda za a tabbatar da manufar gudanar da harkoki tsakanin bangarori daban-daban da kare daidaito da adalci a duniya, da kuma kiyaye muradun bai daya na kasashe masu tasowa.
A nasa bangare, Abdelmadjid Tebboune yana godiya ga goyon baya da Sin ta dade tana baiwa kasarsa, ya kuma yaba rawar da Sin take takawa wajen warware batutuwan da suka shafi Palasdinu da sauran yankunan shiyyar cikin adalci, da sa kaimi ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyyar da duniya baki daya, Yana fatan kara hadin kai da kasar Sin don ingiza huldar kasashen biyu da ma tsakanin Sin da Afrika zuwa wani sabon matsayi, ta yadda zai amfanawa al’umommin bangarorin biyu.
Bayan ganawarsu, shugabannin kasashen biyu sun shaida rattaba hannu kan wasu takardun hadin gwiwa a fannonin aikin gona, da sufuri, da kimiyya da fasaha. Haka kuma kasashen Sin da Aljeriya sun fitar da “Hadaddiyar sanarwar Jamhuriyar Jama’ar Sin da Jamhuriyar Demokaradiyyar Aljeriya”. (Amina Xu)