A yau ne, firaministan kasar Sin Li Qiang ya gana da manzon musamman na shugaban kasar Amurka kan sauyin yanayi John Kerry a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
Li ya bayyana cewa, Sin da Amurka kasashe ne masu muhimmanci a duniya, kuma inganta hadin gwiwar dake tsakaninsu, ba kawai zai amfanawa juna ba, har ma da duniya baki daya.
- Xi Ya Jaddada Gina Kyakkyawar Sin Da Inganta Zamanantar Da Zaman Jituwa Tsakanin Dan Adam Da Muhalli
A nasa bangare John Kerry ya ce, Amurka na fatan alakar kasashen biyu, za ta daidaita.
Bugu da kari, a yau Talata ne mamba a ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma daraktan ofishin lura da harkokin waje na kwamitin kolin JKS Wang Yi, shi ma ya zanta da John Kerry a nan birnin Beijing.
Yayin zantawar tasu, Wang Yi ya ce duniya na bukatar alakar Sin da Amurka ta kasance cikin yanayi na daidaito. Kaza lika ya kamata sassan biyu su aiwatar da matakai masu inganci, su yi aiki tare, don dawo da alakar kasashen biyu kan turba ta gari.
Kaza lika, Wang ya ce Sin a shirye take ta karfafa tattaunawa da tsagin Amurka, ta yadda za a kai ga cimma moriyar hadin gwiwa, da hada kai wajen shawo kan kalubalen sauyin yanayi.
Shi kuwa a nasa bangare, mista Kerry cewa ya yi har kullum Amurka, na nacewa manufar nan ta kasar Sin daya tak a duniya, kuma a shirye take ta karfafa hadin gwiwa da kasar Sin karkashin manufar martaba juna, da warware sabanin kasashen biyu lami lafiya, da kuma hada karfi wuri guda don magance kalubalolin dake addabar duniya, kamar na sauyin yanayi. (Saminu Alhassan, Ibrahim Yaya)