Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a yayin taron manema labaru na yau da kullum Talatar nan cewa, a matsayinta na aminiyar Sudan, gwamnatin kasar Sin za ta samar da taimakon jin kai na gaggawa da darajarsa ta kai kudin Sin Yuan miliyan 10 ga kasar Sudan, domin saukaka matsalolin jin kai. Haka kuma, kasar Sin za ta ci gaba da samarwa bangaren Sudan taimakon jin kai bisa bukatunta.
A game da amincewa da kudurin “Gudunmawar raya kasa don jin dadin daukacin ‘yancin dan Adam” da kasar Sin ta sake gabatarwa a yayin taron kwamitin kare hakkin dan-Adam na MDD karo na 53 kuwa, Mao Ning ta bayyana cewa, amincewa da kudurin ya nuna cikakken buri na bai daya na kasashe masu tasowa.
Dangane da manufar kasar Amurka na takaita sanya hannun jari a kasar Sin, Mao Ning ta ce, har kullum kasar Sin tana adawa da yadda Amurka ke amfani da siyasa a fannonin tattalin arziki, da kasuwanci da fasaha, kuma wannan tsari ba zai amfani kowane bangare ba. (Mai fassara: Ibrahim)