Mataimakin babban magatakardan MDD mai lura da ayyukan wanzar da zaman lafiya Jean-Pierre Lacroix, ya godewa kasar Sin, bisa goyon baya, da taimakonta ga ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD.
Jami’in, wanda ya bayyana hakan yayin liyafar murnar cika shekaru 96 da kafuwar rundunar sojojin ‘yantar da al’ummar kasar Sin, wanda ofishin jakadancin Sin a MDDr ya shirya da yammacin jiya Talata, ya ce cikin shekarun baya bayan nan, kasar Sin na ci gaba da gudanar da hadin gwiwar kut da kut tare da MDD a sassa daban daban, tana kuma goyawa majalissar baya, wajen gudanar da ayyukanta na hadin gwiwa. Kaza lika Jean-Pierre Lacroix, ya ce MDD na fatan ci gaba da karfafa hadin gwiwa da Sin a fannoni masu yawa.
A nasa bangare kuwa, shugaban kwamitin hafsoshi na tawagar zaunannun wakilan Sin a MDD Yin Zhongliang, cewa ya yi rundunar sojojin kasar Sin, ta aike da dakarun wanzar da zaman lafiya, da sojoji kimanin 50,000, domin aiki a sassa har 25 na MDDr, baya ga zurfafa musayar kwarewar ayyukan soji, da na hadin gwiwa da sama da kasashe 150.
Yin ya ce a nan gaba kuma, sojojin kasar Sin za su ci gaba da mara baya, wajen shiga a dama da su, cikin ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD, da sauran sassa masu nasaba da hakan, kana za su gabatar da sabbin gudummawa, a ayyukan wazar da zaman lafiya. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp