Mambobin kungiyar ECOWAS, a ranar Lahadi, sun ba sojojin kasar Nijar wa’adin kwanaki bakwai da su maido da gwamnatin Muhammed Bazoum da aka hambarar kan mukaminsa na shugaban kasa.
Hakan ya biyo bayan wani taro na musamman da shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS suka yi a fadar gwamnati da ke Babban birnin Nijeriya, Abuja, domin tattauna abubuwan da ke faruwa a Jamhuriyar Nijar.
Kungiyar ta amince da Bazoum a matsayin halastaccen shugaban kasar Nijer. Kungiyar ta kuma sanya dokar rufe filaye da kan iyakoki, tare da dakatar da zirga-zirgar jiragen sama na kasuwanci tsakanin Nijar da kasashe mambobin kungiyar ECOWAS.
Da yake sanar da matakin, shugaban hukumar ECOWAS, Omar Touray, ya ce dukkanin hafsoshin tsaron kasashen kungiyar za su gudanar da wani taron gaggawa don tsara dabarun aiwatar da ayyukan soji na maido da Bazoum kan mukaminsa.
Touray ya ce, kungiyar ECOWAS za ta dauki dukkan matakan da suka dace don maido da tsarin mulki a Jamhuriyar Nijar.
“Irin wadannan matakan na iya hadawa da amfani da karfin soji.
“Don haka, hafsoshin sojojin kasashen ECOWAS za su yi taron ganawa cikin gaggawa.”
Da yake sanar da takunkumin tattalin arziki, Touray ya ce, ECOWAS ta amince da “dakatar da duk wata huldar kasuwanci da hada-hadar kudi tsakanin kasashen kungiyar ECOWAS da Nijar.
“Za a dakatar da duk kadarorin Jamhuriyar Nijar a babban bankin gamayyar kungiyar. Za kuma a rufe asusun jamhuriyar Nijar da kamfanonin gwamnati da ke bankunan kasuwanci.”