Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zai yi jawabi ga ‘Yan Nijeriya a ranar Litinin, 31 ga Yuli, 2023 da karfe 7 na yamma.
An umurci gidajen Talabijin da gidajen rediyo da sauran kafafen yada labarai na zamani da su rika yada a shirye-shiryensu.
Mai bawa shugaban kasa shawara na kan yada labarai, Dele Alake, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa d aka fitar ranar Lahadi 30 ga Yuli, 2023.