Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, a ranar Alhamis, ya karbi bakuncin ‘yan mata hudu da aka ceto daga hannun ‘yan bindiga bayan shafe watanni bakwai a hannunsu.
‘Yan Matan na cikin wani faifan bidiyo da ‘yan bindigar suka fitar a makonnin da suka gabata, inda suke rokon Gwamnan da ya taimaka wajen ganin an ceto su. An yi garkuwa da ‘yan Matan ne watanni bakwai da suka gabata akan hanyar Kaura Namoda zuwa Birnin Magaji da ke jihar.
Babban Mataimaki na musaman kan yada labarai na gwamnan Zamfara, Suleiman Bala ne ya bayyyana hakan a wata sanarwa dauke da sa hannunsa da ya raba wa manema labarai a Gusau, babban birinin Jihar.
Bala ya bayyyana cewa, gwamnatin jihar ta damu matuka tun bayan fitar da faifan bidiyon, wanda hakan ya sa aka dauki matakin gaggawa wanda ya kai ga kubutar da ‘yan Matan.
Gwamna Lawal a lokacin da yake karbar bakuncin ‘yan matan, ya gode wa Allah da ya da samun nasarar kubutar da ‘yan Matan da aka yi garkuwa da su.
‘Yan Matan da ake ceto sune: Jamila Yahaya Isa, Aisha Yahaya Isa, Ummulkhairi Musa da UmmulKhairi Sani Umar.