Mahukuntan yankin Taiwan da ke karkashin shugabancin jam’iyyar Democratic Progressive Party wato DPP sun sanar a jiya cewa, mataimakin jagorar yankin Lai Ching-te zai tashi daga Taiwan zuwa kasar Paraguay a ranar 12 ga wannan wata don halartar bikin rantsar da shugaban kasar, kuma zai ziyarci birnin New York da San Francisco a matsayin zangon dake kan hanyar zuwa kasar Paraguay da dawowarsa.
Game da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, Sin ba ta amince da mu’amalar gwamnati tsakanin yankin Taiwan da Amurka ta ko wace hanya ba, kuma ba ta amince ‘yan a-ware na yankin Taiwan su ziyarci Amurka bisa kowane dalili ba, haka kuma ba ta amince Amurka ta goyi bayan ‘yan a-waren Taiwan da aikace-aikacensu na neman ‘yancin kan Taiwan ba. Kakakin ya ce Sin za ta sa ido sosai kan wannan batu, da daukar matakai masu karfi don tabbatar da ikon mulkin kasar da cikakkun yankunan kasar. (Zainab)