Kungiyar agaji ta Red Cross ta kasar Sin, ta ware yuan miliyan 20, kwatankwacin dala miliyan 2.8, domin tallafawa mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a biranen Beijing da Tianjin da lardin Hebei, domin sake tsugunar da su da aiwatar da gyare-gyare.
Bugu da kari, ma’aikatun kudi da na sufuri a kasar Sin, sun samar da kudade da yawan su ya kai yuan miliyan 30, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 4.2, domin gudanar da ayyukan gaggauwa na gyaran titunan da suka lalace, sakamakon mahaukaciyar guguwa, da ruwan sama kamar da bakin kwarya da suka aukawa wasu yankuna biranen Beijing da Hebei.
Kudaden na musamman, za a yi amfani da su ne a matsayin rangwamen kudin da biranen za su kashe, wajen gyaran titunan da suka lalace, a yankin Beijing-Tianjin-Hebei.
Sakamakon mummunan tasirin guguwar mai lakabin Doksuri, wadda ita ce ta biyar da ta auku a bana, yankin Beijing-Tianjin-Hebei na kasar Sin, ya fuskanci mamakon ruwan sama, wanda ya haifar da sanya matakin samar da daukin gaggawa na 2 kan ambaliyar ruwa, tare da ayyana matakin gargadi mai launin ja, wanda shi ne matakin gargadi mafi girma da ake ayyanawa sakamakon aukuwar mamakon ruwan sama.
Tun bayan fara kididdige aukuwar mamakon ruwan sama shekaru 140 da suka gabata, birnin Beijing ya gamu da ruwan sama mafi karfi ne cikin ’yan kwanakin da suka gabata. (Fa’iza Mustapha, Saminu Alhassan)