Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya aike da wasika ga majalisar dattawa inda ya shaida mata cewa ya janye zabin da ya yi wa Maryam Shetty a cikin jerin Ministocinsa.
Kan wannan matakin, Tinubu ya maye gurbin Shetty da Mairiga Mahmud, daga jihar Kano.
Kazalika, shugaban ya kuma kara sunan Festus Keyamo, SAN cikin jerin Ministocin da ya zaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp