Gaskiya sai dai dua’i da kuma godiyan Allah.kin GA sai an je kamfani an siyo GA kara farashin da su kayi saboda tashin Kaya a kasuwa Ka biya Mai Baro ya kwaso ya kawo maka gida,Ka saka cikin freezer ya kankare Ka bayar wa masu sari su kuma suna fadar kudin mota ya Karu Inda suke kaiwa su siyar na da nisa ga kudin mota ya yi tsada ba su samun riba kamar yadda suke samu da.wani Lokacin ma har fadawa su ke yi a ciki sakamakon sun siyar da Kaya sun ci abinci GA kudin mota da ya Karu sai ki ga BA su rage da KO sisi BA.
Ya bambancin cinikin da kike samu ada da yanzu:
Gaskiya sana’a ce da ake samu sosai musamman idan Ka na da kayan aiki wato freezai KO kuma cold room za Ka samu sosai saboda na Gina gidaje da sana’ar nan kuma hatta cold room din da na Fara da guda biyu ne Amma yanzu da taimako Allah Ina da cold room 3 a gida kuma Ina da shago ma na dauki masu tayani siyar da kaya
Ya ya kuke fama da wutar lantarki?
Alhamdulillah muna samun wuta sosai sai dai matsalar su ma NEPA kudin wutan da suke kawo mana yayi yawa sosai don bill wani Lokacin Har 100000 su ke kawowa kin GA shima Yana Kara ja da sana’ar Baya.
Wane kira za ki yi ga mata masu zaman jiran sai an kawo an ba su?
Mata Lokaci ya yi da ya kamata mu tashi mu nemi Abin yi saboda ya na kara wa mace daraja a gun mijin ta tunda ba sai kin jira ba kuma kina taimako shi ne tunda in kin yi abu a gida AI kin toshe baban abu ne tunda ko riga mai kyau aka gan ki da shi za a ce shi ya saya miki.
Wane kira za ki yi wa gwamnati
Ni dai roko na Allah ya kawo mana karshen wannan matsalar kuma su taimaka don rage kudin Fetur jama’a na wahala.