• English
  • Business News
Tuesday, August 12, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Amurka Ta Kasa Tilastawa Kasashen Afirka Su Goyi Bayanta

by CMG Hausa
2 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Amurka Ta Kasa Tilastawa Kasashen Afirka Su Goyi Bayanta

A sales assistant waits for customers at the Huawei Technologies Co. branded booth inside Awolowo glass house in Lagos, Nigeria, on Monday, March 29, 2021. Nigerians are having to contend with the highest inflation rate in four years, the second-highest unemployment rate on a list of 82 countries tracked by Bloomberg, and an economy that’s only just emerged from recession. Photographer: Adetona Omokanye/Bloomberg

Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A shekarun nan, kasar Amurka na ta kokarin keta hakkin kamfanonin fasahohin zamani na kasar Sin irin su Huawei, har ma tana neman tilastawa kasashen Afirka su goyi bayanta, da daina yin amfani da fasahohin Sin. Sai dai wannan yunkuri nata bai yi nasara ba.

Anil Sooklal, manzon musamman na kasar Afirka ta Kudu mai kula da batutuwa masu alaka da nahiyar Asiya da tsarin hadin gwiwa na BRICS, ya yi jawabi a jami’ar KwaZulu-Natal ta kasarsa a kwanakin baya, inda ya ce, kasar Amurka ta matsawa kasar Afirka ta Kudu babbar lamba, don ta daina yin amfani da fasahohi masu alaka da yanar gizo ta sadarwa na kamfanin Huawei na kasar Sin. Sai dai a cewar mista Sooklal, kasarsa ba za ta daina yin amfani da fasahohi da na’urori na kamfanin Huawei ba, saboda “kamfanin ya samar da dubban kwasa-kwasai din horo a kasar Afirka ta Kudu, gami da dimbin damammaki na mika fasahohin zamani, cikin shekarun baya.”

  • Kasar Sin Ta Gabatar Da Korafi Game Da Yunkurin Amurka Na Samar Da Tallafin Soji Ga Yankin Taiwan 

Hakika yunkurin kasar Amurka na dakile kamfanonin Sin ya sabawa ra’ayin da ta daukaka na samun kasuwa mai ‘yanci da ciniki cikin ‘yanci, lamarin da ya nuna cewa, kasar ba za ta ci gaba da bin ka’idoji ba, idan ta ji za a girgiza matsayinta na ‘kasa mafi karfi a duniya’. Kamfanin dillancin labarai na Bloomberg na kasar Amurka ya ba da labarin cewa, don neman zama kan gaba a fasahohin kwaikwayon tunanin dan Adam na AI, da na na’urar latironi ta Chip, da dai sauransu, kasar Amurka na kokarin matsawa sauran kasashe lamba, don su daina hadin gwiwa da kamfanonin fasahohin zamani na Sin. Don neman biyan bukata, har ma kasar Amurka ta fara yada labarin karya, cewa wai kamfanonin Sin na taimakawa gwamnatin kasar Sin satan bayanai, ko da yake ba a iya samar da wata shaidar da za ta goyi bayan wannan zargi ba.

Kasar Amurka tana matsa lamba, da yada jita-jita, amma basa tasiri kan kasashen Afirka. A watan da ya gabata, shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya yanka kyalle don kaddamar da wata sabuwar cibiyar kirkire-kirkire ta kamfanin Huawei a birnin Johannesburg, inda ya yi jawabin cewa fasahohin Sin za su taimaki kasashen Afirka wajen “halarta cikin juyin juya hali na masana’antu karo na 4”. Kana a bara, an kaddamar da yanar gizo ta sadarwa ta 5G a kasar Habasha, bisa fasahohin da kamfanin Huawei na kasar Sin ya samar. A kasar Najeriya kuwa, kamfanin ya gina tashoshin sadarwa kimanin 27500, da wayoyin aika sako ta haske na tsawon kilomita 10000, gami da horar da dimbin matasa da ilimin aikin sadarwa…

To me ya sa matakin da kasar Amurka ta dauka bai samu amincewa daga kasashen Afirka? Dalilin da ya sa haka shi ne domin kasashen Afirka sun san mene ne abun da suke bukata. Burinsu shi ne yin amfani da zarafi na juyin juya hali a fannin masana’antu karo na 4 wajen raya fasahohi na zamani da samun ci gaban tattalin arziki cikin sauri. Don biyan wannan bukata suna neman yin hadin gwiwa da duk wani bangaren dake son hadin kai tare da su, maimakon nuna goyon baya ga wata bisa matsin lambar da aka yi musu. Ra’ayinsu ya yi daidai da maganar da wani masani dan kasar Afirka ta Kudu mai suna Iginio Gagliardone ya fada, wato“duk wani bangaren dake iya samar da fasahohin zamani, zai iya taimakawa kasashen Afirka cimma burinsu.”

Labarai Masu Nasaba

An Samu Karuwar Adadin Kamfanoni Masu Yin Rajista A Yankin HK

Sashen Masana’antun Kirar Motoci Na kasar Sin Ya Samu Gi Gaba A Watan Yuli

Kana wani dalili na daban da ya sa kasashen Afirka kin bin umarnin kasar Amurka, shi ne domin sun san kasar Amurka ta kasa samar musu da abun da suke bukata. Kamar yadda wani masanin ilimi siyasa na kasar Afirka ta Kudu, Jakkie Cilliers, ya fada, “Yadda aka tilastawa kasashen Afirka su goyi bayan wata bai dace da moriyar kasashen ba. Saboda ko da yake ana samun daidaituwa tsakanin huldar kasashen Afirka da Turai da kasar Amurka, da huldarsu da sauran kasashe masu tasowa, irinta kasar Sin, amma na karshen ya fi ciyar da tattalin arzikin kasashen Afirka gaba. Musamman ma ta la’akari da yadda darajar hajojin da kasashen dake kudu da hamadar Sahara ke fitar zuwa kasar Sin ta karu da ninki 10, cikin shekaru 20 da suka gabata. “

A ganina, asalin dalilin da ya hana kasashen Afirka yarda da ra’ayin kasar Amurka shi ne domin ra’ayin kasar tsohon yayi ne. A lokacin da kasar Sin ta gabatar da shawarar tabbatar da ci gaban duniya, inda ta dora muhimmanci kan raya huldar kasa da kasa mai daidaituwa, wadda kuma za ta amfani kowa, don neman biyan bukatar dake akwai a wannan zamanin da muke ciki, kasar Amurka na ci gaba da tsayawa kan manufar “mai da moriyar kanta a sama da ta sauran kasashe”, gami da katsalandan cikin harkokin gida na mabambantan kasashe. Hakika wannan tunani nata na yin babakere a duniya, wanda ya karbe shi tun lokacin yakin cacar baki, ya riga ya tsufa sosai. Ya kamata a rufe shi a cikin littafin tarihi, maimakon a ci gaba da amfani da shi. (Bello Wang)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: AmurkarSin
ShareTweetSendShare
Previous Post

Gwamnan Kano Ya Rantsar Da Mace Ta Farko A Matsayin Babbar Alkalin Alkalai Ta Jiha

Next Post

Sharhi: Rmb Yuan Na Shirin Tumbuke Dalar Amurka

Related

An Samu Karuwar Adadin Kamfanoni Masu Yin Rajista A Yankin HK
Daga Birnin Sin

An Samu Karuwar Adadin Kamfanoni Masu Yin Rajista A Yankin HK

7 hours ago
Sashen Masana’antun Kirar Motoci Na kasar Sin Ya Samu Gi Gaba A Watan Yuli
Daga Birnin Sin

Sashen Masana’antun Kirar Motoci Na kasar Sin Ya Samu Gi Gaba A Watan Yuli

8 hours ago
Tattalin Arzikin Kasar Sin Na Da Makoma Mai Haske In Ji Wani Kwararre 
Daga Birnin Sin

Tattalin Arzikin Kasar Sin Na Da Makoma Mai Haske In Ji Wani Kwararre 

10 hours ago
Sin Ta Kammala Yi Wa Yankuna 5 Na Kare Muhalli Da Halittu Na Kasar Rajista
Daga Birnin Sin

Sin Ta Kammala Yi Wa Yankuna 5 Na Kare Muhalli Da Halittu Na Kasar Rajista

10 hours ago
Masana Kimiyya Na Sin Sun Samar Da Fasahar Sa Ido Kan Cututtukan Da Ake Samu Daga Sauro
Daga Birnin Sin

Masana Kimiyya Na Sin Sun Samar Da Fasahar Sa Ido Kan Cututtukan Da Ake Samu Daga Sauro

13 hours ago
Ofishin Jakadancin Sin A Birtaniya Ya Soki Furucin Kasashen G7 Dangane Da Yankin HK
Daga Birnin Sin

Ofishin Jakadancin Sin A Birtaniya Ya Soki Furucin Kasashen G7 Dangane Da Yankin HK

1 day ago
Next Post
Sharhi: Rmb Yuan Na Shirin Tumbuke Dalar Amurka

Sharhi: Rmb Yuan Na Shirin Tumbuke Dalar Amurka

LABARAI MASU NASABA

Babban Dalilin EFCC Na Yi Wa Tsohon Gwamnan Sokoto, Tambuwal, Tambayoyi

Babban Dalilin EFCC Na Yi Wa Tsohon Gwamnan Sokoto, Tambuwal, Tambayoyi

August 11, 2025
Tireloli Sun Yi Taho Mu Gama, Mutane 4 Sun Jikkata A Titin Zariya–Kaduna

Tireloli Sun Yi Taho Mu Gama, Mutane 4 Sun Jikkata A Titin Zariya–Kaduna

August 11, 2025
An Samu Karuwar Adadin Kamfanoni Masu Yin Rajista A Yankin HK

An Samu Karuwar Adadin Kamfanoni Masu Yin Rajista A Yankin HK

August 11, 2025
Sashen Masana’antun Kirar Motoci Na kasar Sin Ya Samu Gi Gaba A Watan Yuli

Sashen Masana’antun Kirar Motoci Na kasar Sin Ya Samu Gi Gaba A Watan Yuli

August 11, 2025
Shettima Ya Jagoranci Tawagar Gwamnatin Tarayya Don Yi Wa Iyalan Ogbeh Ta’aziyya

Shettima Ya Jagoranci Tawagar Gwamnatin Tarayya Don Yi Wa Iyalan Ogbeh Ta’aziyya

August 11, 2025
Manoma 2 Sun Rasu, 2 Sun Jikkata A Wani Rikicin Filin Gona A Yobe

Manoma 2 Sun Rasu, 2 Sun Jikkata A Wani Rikicin Filin Gona A Yobe

August 11, 2025
Tattalin Arzikin Kasar Sin Na Da Makoma Mai Haske In Ji Wani Kwararre 

Tattalin Arzikin Kasar Sin Na Da Makoma Mai Haske In Ji Wani Kwararre 

August 11, 2025
Sin Ta Kammala Yi Wa Yankuna 5 Na Kare Muhalli Da Halittu Na Kasar Rajista

Sin Ta Kammala Yi Wa Yankuna 5 Na Kare Muhalli Da Halittu Na Kasar Rajista

August 11, 2025
Ku Yaƙi Cin Hanci Ba Ƴan Adawa Ba – ADC GA EFCC

Ku Yaƙi Cin Hanci Ba Ƴan Adawa Ba – ADC GA EFCC

August 11, 2025
Masana Kimiyya Na Sin Sun Samar Da Fasahar Sa Ido Kan Cututtukan Da Ake Samu Daga Sauro

Masana Kimiyya Na Sin Sun Samar Da Fasahar Sa Ido Kan Cututtukan Da Ake Samu Daga Sauro

August 11, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.