Kungiyar ECOWAS ta sanar da karin kakaba wasu takunkumai kan hukumomi da daidaikun mutane da ke goyon bayan gwamnatin mulkin soja a Jamhuriyar Nijar.
Mai magana da yawun shugaba Tinubu, Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan ga manema labarai a fadar shugaban kasa a ranar Talata a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Ya ce, shugaba Bola Tinubu ya umurci mukaddashin gwamnan babban bankin Nijeriya (CBN), da ya aiwatar da sabbin takunkuman da aka kakaba.
Ya kara da cewa, matakan da aka dauka, amincewar daukacin kasashen kungiyar ECOWAS ne da shugabannin kasashensu suka cimma ba wai Nijeriya ce kadai ke aiwatar da takunkuman ba.
A baya dai, ECOWAS ta bai wa gwamnatin mulkin soji wa’adin kwanaki bakwai na dawo da shugaba Mohamed Bazoum kan karagar mulki ko kuma su fuskanci tsangwama ta hanyar kakaba musu takunkumai ciki har da amfani da karfin Soji idan har gwamnatin mulkin sojin kasar ta gaza yin hakan.
Amma sojojin da suka yi juyin mulkin suka yi watsi da barazanar tare da bayyana shirinsu na fuskantar yaki da kasashen da ke karkashin kungiyar ECOWAS.
Ya kara da cewa, babban taron kungiyar ECOWAS da za a yi ranar Alhamis mai zuwa, zai fayyace matsayar Kungiyar ECOWAS dangane da halin da ake ciki a Jamhuriyar Nijar.