Kwanan nan ne shugaban Amurka Joe Biden ya rattaba hannu kan wata doka da ake kira “Dokar aiwatar da yerjejeniyar mataki na farko na shirin kasuwancin Taiwan da Amurka na karni na 21”. Da yake mayar da martani, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a yau cewa, a ko da yaushe kasar Sin tana adawa da duk wani nau’i na mu’amala a hukumance tsakanin kasashen da suka kulla huldar diflomasiyya da kasar Sin da yankin Taiwan na ta.
Kasar Sin ta bukaci Amurka da ta gaggauta soke wannan “doka” kuma kar ta wuce gona da iri a kan hanyar da ba ta dace ba.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya kuma bayyana cewa, kasar Sin na adawa da girke sojojin da Amurka ke yi a kasashe makwabta, tana kuma yin Allah wadai da yada labaran karya da Amurka ke yi domin cimma wannan buri. Kakakin ya kara da cewa, yana fatan kasashen duniya, musamman ma kasashen da ke makwabtaka da kasar Sin, za su yanke hukuncinsu kan hakikanin aniyar Amurka. (Mai fassara: Yahaya)