An gudanar da taron koli karo na biyu na hukumar kula da harkokin tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen Sin da Angola.
A yayin taron na jiya, wanda ministan kasuwanci na kasar Sin Wang Wentao da karamin ministan kula da harkokin tattalin arziki na Angola Jose de Lima Massano suka jagoranta, Wang ya bayyana cewa, karkashin jagorancin shugabannin kasashen biyu, manyan tsare-tsare, hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Angola ya haifar da kyakkyawan sakamako.
Ya ce, a shirye kasar Sin ta hada kai da Angola wajen tsara dabarun inganta hadin gwiwa a fannin tattalin arziki da cinikayya, da kara habaka hadin gwiwar cinikayya da zuba jari, da karfafa nasarorin da aka cimma a hadin gwiwar samar da ababen more rayuwa, da fadada cudanya a fannonin makamashi, da ma’adinai, da masana’antu, da aikin gona, da kamun kifi.
Bugu da kari, ya bayyana manufar samar da ci gaba mai inganci a fannin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen biyu, da sa kaimi ga inganta dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Angola.
A nasa bangare kuwa, Massano ya ce, kasar Sin sahihiyar aminiyar hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya ta Angola ce. Bangaren Angola na da sha’awar yin aiki kafada da kafada da kasar Sin, domin kara karfafa hadin gwiwa mai inganci a fannin tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen biyu wato Sin da Angola.
Massano ya kara da cewa, Angola na maraba da karin kamfanonin kasar Sin da su zuba jari da ma kafa kansu a kasar Angola, da shiga a dama da su wajen aiwatar da tsarin habaka tattalin arzikin kasar, da zurfafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen biyu. (Ibrahim Yaya)