An kai karar Mai Martaba Sarkin Ilorin, Dakta Ibrahim Sulu-Gambari kotu bisa zarginsa da hana mabiya Addinin Olokun gudanar da shagalin bikin gargajiya na Isese a garin Ilorin da ke a jihar Kwara.Â
Wani Lauya mazaunin Jihar Legas kuma mai rajin kare ‘yancin dan Adam, Malcolm Omirhobo ne ya shigar da kara a gaban babbar kotun Kwara.
- Ganduje Ya Bukaci ‘Yan Majalisar Dokokin APC Su Goya Wa Abba Baya
- Cinikin Maguire daga Manchester United Zuwa West Ham Ya Lalace
Malcolm wanda ya danganta kansa a matsayin mabiyin Addinin Olokun ya hakikance da cewa, matakin na Sarkin na hana bikin gargajiya na Isese, ya sabawa ‘yancin dan Adam na gudanar da Addininsu kamar yadda sashe na 38 na kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 ya tanada.
Kazalika, Omirhobo a cikin kararsa, ya nemi kotun da ta ayyana cewa, garin na Ilorin shi ma yanki ne na Nijeriya kamar kowane yanki da ke dauke da mabiya Addinai daban-daban da mabiya al’adu wanda bisa wadannan hujjojin, Sarkin bai da wani karfin ikon hana gudanar da bikin gargajiya a garin Ilorin da ke jihar Kwara.
Bugu da kari, Omirhobo ya kuma bukaci kotun da ta dakatar da Sarkin ko wani hadiminsa daga cin zarafinsa, tursasawa da kuma hukunta mai karar daga fadin ‘yancinsa da kuma gudanar da shagalinsa da kuma mabiya Addinin na Olokun wajen gudanar da bikin gargajiyar cikin kwanciyar hankali da lumana a Ilorin.