A jiya ne, babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG da kungiyar kawancen kafofin rediyo na Afirka, suka gudanar da taron dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar kafofin watsa labaru na Sin da Afirka na shekarar 2023 a Nairobin kasar Kenya.
Taken taron shi ne “Neman fahimtar juna tsakanin al’ummomi da samar da kyakkyawar makoma”, inda mataimakin darektan sashin kula da harkar fadakarwa na kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin kuma ministan al’adu da yawon shakatawa na kasar, Hu Heping, ya halarci taron tattaunawar tare da gabatar da jawabi.
A nasa bangare, shugaban kamfanin CMG Shen Haixiong shi ma ya yi wani jawabi ta kafar bidiyo. Yayin da shugaban kungiyar kawancen kafofin rediyo na Afirka Grégoire Ndjaka, da jakadan kasar Sin dake kasar Kenya Zhou Pingjian, da shugabannin hukumomin kafofin watsa labaru na wasu kasashe 27 dake nahiyar Afirka, da suka hada da Kenya, da Afirka ta Kudu, da Najeriya, wadanda yawansu ya zarce dari daya, gami da wasu masana, da wakilan kamfanonin Sin da na kasashen Afirka sun halarci taron a zahiri ko kuma ta yanar gizo.
Shugaban kamfanin CMG, Shen Haixiong, ya bayyana a cikin jawabinsa cewa, ya kamata a taimaki kasashen Afirka da kasar Sin wajen samun wadata da cigaba tare, da yada fasahohin da aka samu ta hanyar zamanantar da fannin al’adu na dan Adam.
Ya ce, kamfanin CMG yana son hada kai da abokan huldar kasashen Afirka, don sa kaimi ga samun ci gaban Sin da Afirka, da nuna kyawawan abubuwa masu burgewa da al’adun bangarorin 2 suka kunsa, da ba da gudummawa ga yunkurin gina al’ummar Sin da Afirka mai kyakkyawar makoma ta bai daya ta sabon zamani. (Zainab)