“Daga filin motoci zuwa kofar gidanmu, launin sama ya canja daga shudi zuwa baki. Duk inda muke gani gobara ce, amma ba mu san me ya faru ba. Babu wani gargadi ko kashedi.”, in ji wata mazauniyar garin Maui na jihar Hawaii, Akanesi Vaa, wadda ta tsira daga bala’in.
Ya zuwa ran 16 ga wata, wannan gobara da ba a taba ganin irinta a cikin karni ba, ta halaka mutane a kalla 110, mutane fiye da dubu kuma sun bace. An ce, Hawaii na da tsarin gargadi mai inganci dake shafar duk fadin jihar, amma mazauna sun ce, ba su ji ko ga wata alamar gargadi ba.
Ban da haka kuma, bayan aukuwar bala’in, gwamnatin wurin ba ta dauki matakan da suka dace ba, kuma ba ta tura sojoji ko rukunonin kashe wuta zuwa wurin don kwashe mutane ba. Haka kuma, gwamnatin Washington ba ta dauki matakan samar da agaji cikin lokaci ba, jama’a ne kawai suka hada kansu don ceton juna. Wannan shi ne muhimmin dalilin da ya daga adadin asarar rayuka.
Lokacin da ake fama da bala’in, shugaban kasar Amurka Biden yana hutu, yana more rayuwa a gabar teku. Yayin da aka yi masa tambaya game da asarar da aka tafka a bala’in, ya ce: “Ba zan ce kome ba”. Sai bayan da ya sha suka, sannan ya ce, zai kai ziyara Hawai tare da matarsa.
Da ganin haka, mazaunan wurin suka fusata matuka, inda suka ce: “Yayin da muke matukar bukatar agajin gwamnatin bayan aukuwar gobara, ina take? Mun yi fushi sosai, mun rasa gidajenmu, gobara ta cinye garinmu.”
Wannan gobara ba ma kawai ta kone gidaje da dukiyoyin jama’a ba, har ta kashe mutane da dama, ta kuma halaka amincewar da jama’a suka yi da gwamnatin Amurka. (Mai zana da rubuta: MINA)