Mutane da dama idan suka ji ance ‘typing’ (rubutu) mun fi jingina kalmar da rubutun haruffa kadai, a kwamfuta, typing ya kunshi duk wani aiki da zai bukaci amfani da ‘yan yatsunka, saboda haka tabbas ba iya rubutun haruffa ne yatsunmu za su iya ba, akwai abubuwa kamar haka: rubutun Lambobi, haruffan Yaruka kamar Larabci, Farisanci da sauransu.
Za mu fahimci ma’anar ‘Word processing’ ta hanyar bada misalan kayan rubutu, musamman Microsoft word office, wanda aka fi sani da Microsoft word (MSword), Microsoft Spreadsheet (MSedcel) da kuma Microsoft powerpoint (MSppt).
Dukkansu ana samunsu a wayoyin hannu. Akwai makamantansu an kirkiresu ne domin su maye guraben na kwamfuta. Akwai application a ‘play store’ WPS Office, ma’anarsa (Writer, Presentation and Spreadsheet) wannan Application ya kunshi dukkan abubuwan da ake bukata wajen rubutu. Hakan ne ya zame mana dalilin yin amfani da shi wajen yin cikakken bayani a kansa a nan gaba.
Yaya Application din WPS Office yake?
Shi ma dai application ne kamar Ms-Office yana dauke da muhimman tsarurruka na rubutu irin wanda kwamfuta ke dasu, kuma da sune za a samu damar yin rubutu a wayar salula, sune kamar haka:
Microsoft document (.docd) : wanda ake rubutu kuma ayi print.
Microsoft Excel (.xlsd) : wanda ake lissafi da shi misali a makarantu, ma’aikatu ko masana’antu.
Microsoft PowerPoint (.ppt) : wanda ake yin rubutu mai motsi da shi.
A nan gaba zamu kawo yadda ake amfani da kowanne daya daga cikinsu.
Yadda ake sauke WPS Office a kan wayar hanu.
Da farko za a shiga cikin google play store sai a rubuta WPS office a cikin akwatin bincike (search box). Sai a danna search, misalai za su fito sai a zabi daidai da abin da ake nema kuma a sauke shi a cikin waya din (download).
Sai a bude shi Application din za a ga alamar tarawa (+) ta lissafi daga bangaren dama a kasa.
Zabi zai fito sai a zabi abin da ake so kamar haka:
Na farko shi ne zai baka damar ka yi rubutu, kamar wasika (word) Kenan.
Na biyunsa kuma da shi ake rubutu mai motsi kamar haka. (power point) Kenan.
Na ukunsa da shi ake lissafi (Spreadsheet/Edcel).
A shafi na gaba sai a zabi blank page a yi rubutu a gama, idan an gama sai a bawa rubutun suna kuma a yi Sabing dinsa kamar haka:
Ga wadanda suka saba typing a kan kwamfuta sai su yi amfani da wayarsu cikin kwanciyar hankali a duk lokacin da suka ga dama. Wato hanyoyin yin sabing din, iri daya ne da na kwamfuta.
Menene Amfanin sauke WPS Office a kan waya?
Za a iya cewa karin samun hanyar sakakawa ne, domin kuwa za ka iya yin duk rubutun da kake so a wayarka, ba sai ka dauko kwamfuta ba. Idan kuma ma ba ka da Kwamfuta bai zama wajibi sai ka mallaketa ba, musamman idan ba ka da halin saya.
Idan akwai WPS Office a wayarka, ba ka da bukatar kaiwa wajen da za a caje ka kudi domin a yi maka rubutu (typing).
Idan akwai WPS Office a wayarka a ko da yaushe kuma a ko ina kake za ka iya ciro wayarka ka yi rubutu, ba kamar kwamfuta ba wadda dole sai kabje gida ko café ko wani wajen da za ka samu wuri ka zauna, sannan ka zauna ka yi rubutu wanda hakan ba karamin cin lokaci ba.
Kamar wadanne abubuwa za a iya yi da WPS Office?
– Rubuta Assignment.
– Rubutun wasika.
– Hada bayanan neman aiki ‘Curriculum bitae’ (CB).
– Hada katin gayyatar taro, biki ko suna (invitation card).
– Letter heading.
– Hada lissafin kudi.
– Daukar sunan Ma’aikata (employee list).
Tsara lissafin biyan ma’aikata kudin aiki (Employee salary manager).
– Hada bideo ko rubutu mai motsi (Text Animation).