Gwamnatin Jihar Katsina ta kammala dukkanin shirye-shirye domin horas da wasu dakaru na musamman da za su taimaka wa jami’an tsaro wajen magance matsalar tsaro a yankunan da matsalar tsaro ta yi kamari.
Kwamishinan ma’aikatar tsaro da al’amuran cikin gida na Jihar Katsina, Hon. Nasiru mu’azu Danmusa ne ya tabbatar da hakan a wajen taron manema labarai bayan kammala zaman majalisar zartaswar jihar karkashin jagorancin gwamnan Malam Dikko Umar Radda.
Kamar yadda kwamishinan ya bayyana, matasan da za a dauka za su samu ingantaccen horo na yadda za su gudanar da aiki cikin tsari a yankunansu, inda ya bayyana cewa kowane matashi daga cikin wadanda za su karbi horon an zabo shi ne daga yankin da ya fito.
Ya ce bayan sun samu horon za a tura kowannensu a yankin da ya fito domin su hadu tare da jami’an tsaro da nufin tunkarar matsalar tsaro domin kawo karshenta.
Nasiru Danmusa ya bayyana cewa tuni gwamnatin jihar ta amince da fitar da kudi domin tanadar kayan aikin da suka wajaba wajen kaddamar da dakarun na cikin gida wadanda za su yi aikin maido da tsaron da zaman lafiya a yankuna takwas da ke fama da matsalar tsaron a Jihar Katsina.
Ya kara da cewa hakan wani bangare ne daga shirye-shiryen da gwamnatin jihar ke yi wajen kokarin ganin al’ummar sun zauna lafiya domin ci gaba da gudanar da harkokin tattalin arzikinsu cikin kwanciyar hanlali, musamman sana’ar noma da kiwo da ke zaman babbar hanyar da al’ummar jihar ke dogaro da su. I