Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba a ranar Alhamis suka kai hari tare da kashe jami’an hukumar hana fasa gwabri ta kasa wato Kwastam su biyu a jihar Kebbi.Â
A wata sanarwar da mai rikon kakakin hukumar reshen jihar, Mubarak Mustapha ya fitar, ya ce, jami’an su na kan aikin sinitiri ne bayan samun labarin cewa wasu fasa gwabri na cin karensu babu babbaka a kan hanyar Daki Gari Koko ne wasu ‘yan bindiga dauke da muggan makamai suka bude musu wuta a lokacin da suke bakin aiki.
- Gwamnatin Katsina Za Ta Horar Da Matasa Domin Taimaka Wa Jami’an Tsaro
- Gwamnatin Kaduna Ta Yi Murnar Sake Dawo Da Aikin Hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Zariya
“A yayin musayar wutan sun kashe jami’an Kwastam reshe jihar Kebbi biyu.”
Kwanturolan hukumar a jihar Kebbi, Ben Oramalugo, ya nuna matukar kaduwarsa bisa kashe masa jami’ai, ya kuma umarci a gaggauta kaddamar da bincike domin ganowa da kamo makasan domin gurfanar da su.
Oramalugo wanda ya ziyarci iyalan jami’an da aka kashe, ya jajanta musu tare da fatan Allah ba su hakuri. Ya kuma tabbatar musu cewa jinin ‘yan uwansu ba za su tafi haka nan ba.
Tunin dai aka yi jana’izan mamatan kamar yadda addinin musulumci ya tanadar.
Yayin da ke tir da allawadai da kisan na Alhaji Kabiru Shehu da Abdullahi Muhammad dukkaninsu jami’an Kwastam mash mukamin Isifektas ya bukaci jama’a da suke taimaka wa Kwastam da bayanan masu fasa gwabri da ‘yan ta’adda domin dakile aniyarsu.
Duk da kisan na jami’an su, ya bada tabbacin cewa za su cigaba da dakile aniyarsu masu fasa gwabri a fadin jihar.