Matar sufeton ‘yan sanda, Francis Adekunle a ranar Talata ta bayyanawa mai shari’a Hakeem Oshodi na babbar kotun jihar Legas da ke Ikeja yadda abokin mijinta, Sajan Ukeme Asuquo ya kashe mijinta da adda sabida wata ‘yar karamar takaddama a tsakaninsu.
Misis Itunnu Adekunle, wacce ta ke bayar da shaida a shari’ar Kan wanda ake zargi da kashe mijinta, ta yi ikirarin cewa Asuquo ya aikata laifin ne bayan da mijinta ya shiga tsakanin sabanin da ke tsakaninta da Wanda ake karar shekaru biyu da suka gabata.
Gwamnatin jihar Legas dai na tuhumar wanda ake kara ne a kan tuhuma daya na kisan kai wanda ya sabawa sashe na 223 na dokar manyan laifuka, Ch. C17, Vol.3, Dokokin Jihar Legas, 2015.
Asuquo, wanda ke aiki da sashin yaki da masu tsafe-tsafe na rundunar ‘yan sandan jihar Legas, ya kai wa Sufeto Adekunle wanda ke aiki a sashin kariya na musamman, Ikeja, hari da adda a harabar gidansu da ke 1 Oyedeji Close, Agbelekale a unguwar Aboru a Legas. , inda suke zaune da iyalinsu.
Misis Adekunle ta shaida wa kotun cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 8 na daren ranar 4 ga watan Yuni, 2020.