A ranar Laraban nan ne firaministan kasar Sin Li Qiang ya yi karin haske kan matsayin kasar Sin game da batun zubar da ruwan dagwalon nukiliyar Fukushima ta kasar Japan cikin teku, ya kuma yi kira ga kasar Japan da ta dauki matakin da ya dace.
Da yake jawabi a taron koli na ASEAN da kasashen Sin da Japan da Koriya ta kudu karo na 26, Li ya ce, zuba ruwan dagwalon nukiliyar cikin teku ya shafi yanayin muhallin tekun duniya da kuma lafiyar mutane.
Ya kuma yi kira ga kasar Japan da ta sauke hakkin da ke kanta na kasa da kasa da aminci, da tuntubar makwabtanta da masu ruwa da tsaki yadda ya kamata, da kuma kula da batun ruwan dagwalon nukiliyar ta hanyar da ta dace. (Yahaya)