Shugaban kasa Bola Tinubu ya aike da ta’aziyyarsa ga iyalai da dalibai da kuma abokan fitaccen malamin addinin Musulunci Sheikh Abubakar Giro Argungu wanda Allah Ya yi wa rasuwa a ranar Laraba.
Shugaba Tinubu a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale ya fitar, ya bayyana rasuwar jagoran addinin a matsayin wani babban rashi ga kasa.
“Za a dade ana tunawa da Muryar Sheikh Giro Argungu a tsawon shekarun da ya yi na yada addinin Musulunci da kuma ayyukan da ya yi a kungiyar Musulunci ta JIBWIS, inda ya taba rike mukamin Shugaban Kwamitin Ayyuka a kungiyar, ya ba da gudummawa matuka wajen jagorantar ayyukan raya kasa,” in ji shi.
Shugaban ya ce, za a yi kewar Sheikh Giro matuka sabida jajircewarsa na rashin tsoro ga bayyana gaskiya ga shugabanni wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu ga ‘yan kasa.
Shugaban ya kuma jajantawa iyalai, gwamnati da al’ummar jihar Kebbi, da al’ummar Musulmin Nijeriya, bisa wannan babban rashi da aka yi, tare da addu’ar Allah ya jikan Malamin da rahama