Assalamu alaikum masu karatu barkammu da sake haduwa da ku a cikin shirin namu mai farin jiki da albarka na Ado da Kwalliya a wannan mako.
A yau kuma shafin namu zai yi bayani ne akan yadda uwargida za ta yi amfani Kokumba wajen gyara jiki.
- Share Fagen Gasar Kofin Duniya; Messi Ya Zura Kwallo A Ragar Ecuador
- Kasar Sin Na Marawa AU Baya Wajen Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya
Ga abubuwan da Uwargida za ta tanada idan za ta hada wannan hadi na gyaran jiki:
Kokumba, Lalle da Zuma
Da farko za ki samu Kokumbarki ki wanke ta sannan ki yayyanka ta yadda za ki makade ta a blender ta yi laushi sosai, sai ki samu wata roba ki dauko rariya ko matar kadi duk daya ne ki tara a cikin robar nan, sai ki dauko Kokumbar da kika malkada ki zuba a cikin rariya ki tace ruwan Kokumbar dusa a cikin rariyar kamar de yadda za ki tace koma mene ne na ruwa haka yake za ki gan shi sai ki dauko lallenki amma lallan nikansa ya yi laushi sosai da zuma sai ki debi lallen daidai yadda za ishe ki ki zuba dan zuma ki gauraye shi, sannan ki kwaba shi da ruwan Kokumbar za ki yi shi ne da dan ruwa-ruwa kar ya yi tauri yadda za ki shefa jiki da shi sai ki bar shi ya dan yi kamar minti biyar zuwa goma haka saboda ya dan jiku zai fi yi sosai.
Sannan sai ki shafa shi kamar yadda ake dilka haka za ki shafa shi idan ya dan yi kamar minti 30 zuwa awa daya sai ki murje shi sannan ki wanke da dan ruwan dumi.
Habba mana Uwargida zo ki ga yadda fatarki za ta yi subul-suuul za ki yi kyau ki yi sheki ki yi laushi fatarki ta yi santsi sai kinbani labari yadda kika gani.