Kasar Senegal, ita ce kasa ta farko a yankin yammacin Afirka da ta sa hannu kan shawarar ziri daya da hanya daya tare da kasar Sin. Yayin da shugaban kasar Senegal Macky Sall yake hira da wakilin babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG, ya bayyana cewa, kasar Senegal ta kulla kyakkyawar dangantaka da kasar Sin, wadda ta zama dangantakar samun moriyar juna da kuma mai ma’ana sosai.
Shugaba Sall ya ce, a cikin ayyukan more rayuwa da aka gina a kasar Senegal, ciki har da tagwayen hanyoyin mota, da manyan abubuwan more rayuwa, da filin kokawa na kasar, da wuraren adana ruwa a yankunan karkara, da sabon yankin masana’antu da sauransu, muddin kasar Senegal ta yi hadin gwiwa tare da kasar Sin wajen gina su, za a iya kammala su cikin gajeren lokaci, wannan ya taimaka wajen zamanintar da kasar Senegal. (Zainab)