Wata kotun shari’a a jihar Kano a ranar Talata ta bayar da umarnin tsare wani dan kasuwa mai shekaru 35 a gidan gyaran hali kan zargin yin barazanar sace dan dan uwansa.
Rundunar ‘Yansandan ta gurfanar da da matashin da ke zaune a unguwar Alfindiki Quarters, Mandawari a karamar hukumar Municipal a Kano, inda ake tuhumarsa da aikata laifi da ganganci da kuma tsoratarwa.
- Zabe: Kotun Kano Ta Kwace Kujerar Datti Ta Baiwa Iliyasu Kwankwaso
- Kotun Sauraren Kararrakin Zabe Dan Majalisar Wakilai A Kano Ta Tabbatar Da Nasarar Kofa
Alkalin kotun, Malam Umar Lawal-Abubakar wanda ya bayar da umarnin, ya dage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 25 ga watan Satumba.
Tun da farko, dan sanda mai shigar da kara, Insp Abdullahi Wada, ya shaida wa kotun cewa wanda ya shigar da kara, Zahradeen Baba, wanda dan uwa ne ga wanda ake kara ya kai rahoton lamarin a ranar 8 ga watan Satumba a ofishin ‘Yansanda na Mandawari da ke Kano.
Wada ya ce wanda ya shigar da karar ya ruwaito cewa wanda ake kara ya yi barazanar sace dansa idan mai karar ya ki biyan kudin da yake binsa bashi.
Mai gabatar da kara ya ce laifin ya ci karo da tanadin sashe na 158 na kundin laifuffuka.
Lokacin da aka karanta wa wanda ake tuhuma tuhumar, ya musanta aikata laifin.