Colin Patrick Mackerras, wani mai nazarin Sin na kasar Austriliya. A cikin kimanin shekaru 60 da suka gabata, ya sha ziyartar kasar Sin, kuma ya yi bitar abubuwan da ya gani a cikin kasar, kana ya gabatar wa duniya kasar Sin bisa gaskiya.
A cikin watan Nuwamba na shekarar 2014, Mackerras ya gamu da shugaban kasar Sin Xi Jinping, wanda ya kai ziyara kasar Austriliya. Shugaba Xi ya ce, “farfesa Mackerras ya bayyana yanayi na gaskiya na kasar Sin, inda ya gina wata gada ta sada zunmunta tsakanin jama’ar kasashen biyu.”
Mackerras ya taba zuwa wurin da Xi Jinping ya taba aiki yayin da yake matashi, ya ce, “Na taba zuwa yankin Yan’an sau biyu, karo farko shi ne a shekarar 1965, sannan a shekarar 2018. Na ga yadda zaman rayuwar al’ummun yankin Yan’an ya samu babbar kyautatuwa.
Yanzu al’ummun yankin suna farin ciki tare kuma cike da imani. A ganina, kawar da kangin talauci gagarumin ci gaba ne da aka samu, inda shugabanci mai inganci ya taka muhimmiyar rawa, a ganina shugaba Xi ya yi kokari matuka wajen cimma wannan nasara.” (Safiyah Ma)